YADDA AKA YIWA MANZON ALLAH (SAWA) SIHIRI
YADDA AKA YIWA MANZON ALLAH (SAW) SIHIRI
YADDA AKA YIWA MANZON ALLAH (SAW) SIHIRI._______________________
Da gaske ne Sihiri yana iya kama kowa, har Annabin Allah?.
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruqiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على النبي الكريم.
Wasu mutane suna ganin cewar sihiri ba zai iya kama su ba, tunda dai sun yi imani da Allah kuma suna Azkar tare da zama cikin tsarki.
Har da akwai masu inkarin tasirin sihiri ko shigar Aljani jikin mutum.
Ayoyin Alqur'ani, sun nuna cewa lallai sihiri yana tasiri da iznin Allah, haka nan sunnah ta nuna cewa, tsananin rikonka da addini, ba shi ke baka tabbacin cewa sihiri ba zai yi tasiri akanka ba, saidai kawai ka nemi kariya a wajen Allah.
Karanta wannan qissa, zaka fahimci cewa duk tsarkinka, duk kusancinka da Allah, sihiri zai iya tasiri akanka amma da iznin Allah.
Ga yadda qissar ta zo a ruwayoyi masu yawan
gaske.
Yahudawa sun hada baki da wani yaro Bayahude
da yake shiga gidan Manzon Allah, su ka ce ya
samu matajin kan Manzon Allah (SAW) ya cicciro
musu gashin kan Manzon Allah (SAW) daga jiki
kuma ya ďan kakkaryo musu kan matajin
Haka kuwa akayi.
Bayan yaron ya kai musu sai suka haďa sukay wa
Manzon Allah (SAW) sihiri da shi.
Nana A'isha (RA) ta ce " Manzon Allah (SAW) ya yi
rashin lafiya mai tsanani. Har ta kasance sai ya
dinga ganin kamar ya aikata wani abu alhali kuma
be aikata ba.
Ta ce wata rana yana daki na da daddare, yana ta
addu'a, Sai ya kwalla min kira ya ce "Albishirinki
ya A'isha, Allah ya sanar da ni abinda ke damu
na"
Ya ce "Mala'iku biyu ne suka zo min, daya ya
tsaya a saitin kaina, dayan kuma a saitin kafa ta.
Sai na saitin kafar tawa ya ce da na saitin kan
nawa "Me yake damun wannan mutumin ne? "
Sai ya ce masa "An yi masa tsibbu ne"
Sai ya ce "Meye tsibbu? "
Sai ya ce "Sihiri kenan"
Sai ya kuma ce masa "Wa yay masa sihirin? "
Sai ya ce " Wani Bayahude ne mai suna Labiydu
binil A'asam, daga qabilar Baniy Zariyqin.
Sai ya sake ce masa " To yanzu ina (aka binne)
asirin? "
Sai ya ce "A cikin rijiyar Zarwana."
Daga nan sai Manzon Allah (SAW) ya aika Ammar
bin Yasir da wasu mutane, su ka je rijiyar. Sai
suka shiga cikinta, ruwan rijiyar gaba ďaya ya
koma ja saboda bala'in sihiri. Suka kwashe ruwan
rijiyar, sai suka samu an danne asirin ne da wani
katon dutse. Suka dauke dutsen sannan suka fito
da Kullin sihirin.
Da suka kawo wa Manzon Allah (SAW) sai ya
warware shi, sai ga shi ashe an hada shi ne da
hudar ÿaÿan dabino namiji, masu kama da kan
shaidanu. An yi qulle-qulle ne har guda goma sha
daya.
Sai Allah Madaukakin Sarki ya saukar masa da
surorin Falaqi da nasi. Falaqi aya biyar Nãsi aya
shida, goma sha daya kenan. In yakaranta duk aya
daya sai ya tofa a qulli daya, sai qullin ya kwance
da kansa, har dai ya gama gaba daya. Daga nan
sai aka qona layoyin aka binne. Sai Manzon Allah
(SAW) ya samu lafiya, kamar bai ta6a yin cuta ba.
Saidai an ce akwai wata jijiya a idonsa wadda idan
ya shiga halin damuwa sai a ga ta fito ta yi ja,
kuma haka na faruwa ne bayan an yi masa
wannan Asirin.
Mai son ganin wadannan Hadisai ka iya duba
Littafin Šahiyhul Bukhãriy, Kitãbuť ťubbi, Bãbus
sihri, hadisi mai lamba ta 5763.
Sauran 6angarorinsa kuma :- 5766, 5765, 3268,
3175.
Tuhfah:- 16928, 17022, 17134, 17145.
Kuma wannan hujja ce mai karfi da ke nuna cewa
ana yin sihiri don a cutar da mutum. Sannan
babban darasi ne da ke nuna cewa ko kai wanene,
komai girmanka, komai tsarkin ka komai
matsayinka agun Allah za a iya yi ma Asiri kuma
ya kama ka.
Sannan hujja ce da ke nuna cewa lallai ana iya
karya sihiri bayan an yi shi kuma wanda akay wa
ya samu lafiya.
Da akwai addu'o'i na Manzon Allah (SAW) da
ayoyin Alqur'ani da kuma ingantattun magunguna
daga bakin Manzon Allah (SAW) da ake amfani da
su wajen karya sihiri da lalata shariin Aljanu,
wadanda mun sha yin bayani akansu lokuta da
yawa. Haka nan da addu'o'i na neman kariya daga
sharrin masu yin tsafi da masu yin sihiri.
.
Ya Allah ka kare mu da kariyarka kuma katsare
mu da tsarewarka.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
.
bashirhalilu1989@gmail.com
.
bahirhalilutarbiyyahislamiyyah@fb.com
.
Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Comments
Post a Comment