HUKUNCIN YIWA ALJANU YANKA. YANKA DABBOBI BISA UMARNIN ALJANU.


HUKUNCIN YANKA WATA DABBA DON NEMAN LAFIYA. 

Shin ya halatta idan mutum yana da matsalar jinnu a yanka musu wata dabba don su rabu da shi?. 

Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah,  masu yin Ruq'yah da harhahada magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على النبي الكريم. 

Ya riga ya zama sanannen al'amari cewa,  mafi yawancin wadanda suke fama da lalura irin ta jinnu wani lokacin Aljanun sukan nemi cewa a yanka musu wata dabba, za su bar jikin mutum. 

Misali,  wani Aljanin zai ce a yanka Baqin Bunsuru ko Farar Kaza, idan akay haka zai fita daga jikin mara lafiyar. 

Akwai Aljanin da zai yi bayanin cewa,  an yi ciniki da shi akan ya shanye jinin jikin wannan mutumin ko wannan matar,  to amma ya yarda ay sulhu,  a bashi jinin wata dabbar yasha,  don a fanshi rayuwar mutumin. 

YADDA YANKAN YAKE KASANCEWA. 

Wani Aljanin zai ce a samo Qadangare,  a kwankwatse kansa,  a tsiyayar da jinin a qasa. Wani zai ce a siyo kaza,  a tsige mata kai,  a yar,  har ta mutu. Wani kuma zai ce a samo baqin bunsuru,  a yanka shi ta qeya. Wasu ma sukance a siyo wata dabba a daureta ba abinci, har ta mutu. Suna ma cewa a siyo wata dabba a binneta da ranta har ta mutu. Da dai nau'o'i kala-kala. 

Mafi yawa daga cikin sharadin yankan,  za a ce kada a ambaci sunan Allah. 

Sukan fadi yadda za ay da naman dabbar,  ko su ce a je a zuba a gidan tururuwa,  ko a rabawa yara qanana ko kuma su ce mara lafiyar ya cinye,  ko kuma a soya a baiwa Aljanin ya tafi da shi. 

Ba masu rashin lafiyar jinnu ne kawai Aljanu suke sa su yin yanka ba, duk wanda yake da wata bukata a wajen Aljanu,  to sukan umarce shi ya yanka wata dabba,  ko ya daure,  ko ya binne. 


ME YASA ALJANU SUKE SAKA MUTUNE  YANKAN DABBOBI? 

Mafi yawan Aljanun da suke cewa a yanka musu dabbobi ba musulmai bane. Duk da akan samu masu cewa su Rauhanai ne kuma su sa adinga yanke-yanken dabbobi amma maganar gaskiya arna ne kawai. Na kawo cikakken bayani akan Rauhanai `yan cuwa-cuwa,  acikin rubutuna mai taken SUWAYE RAUHANAY?. Mai bukata zai iya duba shafi na na facebook, ko email address bashirhalilu1989@gmail.com


Daga cikin dalilan da suke sawa su ce ay musu yanka. 

1- Idan suka ga iyalin mara lafiyar suna zuwa suna lalla6a su,  har ma suna tambayarsu cewa su fadi abinda suke so ay musu,  su bar jikin mara lafiyar. To sai suyi ta lissafo abubuwa suna cewa ayi musu,  ciki har da yanka,  ko siyen alewa,  wasu Aljanun ma har abinci suke sawa a dafa musu,  su ci,  sannan su tafi. 

2- Idan Aljanu suka ga an je wajen mai maganin da bai san abinda yake ba ko kuma wajen mai aiki da Aljanu,  to sai su ce ay musu yanka.  Karshe ma mai maganin za su dinga baiwa umarni,  shi kuma yana gayawa mai lalurar. Watakila ma shi za a kaiwa dabbar ya yanka. (Na yi cikakken bayani akan Aljanu masu yaudara mai ruq'yah,  acikin posting dina mai take "JINNUL JALAB WATTAHDEER" ku duba shafina na facebook). Don haka za su dinga yaudarar mai maganin,  yana sawa anay musu yanka. 

3- Aljani ya san Dan-Adam ya fi shi daraja,  don haka yana jin dadi yaga yana baiwa `Yan-Adam umarni suna bi. Saboda haka ne zai dinga bada umarnin cewa ayi masa yanka ko ay masa sadaka. 

4- Wani Aljanin ya san hukuncin yin yanka a musulunci shirka ne,  don haka yake so yasa musulmi ya aikata shirka. 

5- Da akwai Aljanu mayu,  mashaya jini,  kamar Tabriyqul jinni. Suna sawa ne ayi yanka don su samu jinin da za su sha. 


HUKUNCIN YIWA ALJANU YANKA A ADDININ MUSULUNCI. 


 Allah Madaukakin Sarki Yana cewa acikin Suratul An'ami:


بسم الله الرحمن الرحيم 
 {قُلْ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ - لَا شَرِيكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ} [الأنعام: 162 - 163

Ma'ana: _Ka ce,  lallai sallahta, da YANKANA da rayuwata da mutuwata,  duk na miqa su ga Allah,  Ubangijin halittu,  shi kadai,  ba wani abokin tarayya a tare da shi._

Sharhi: Daga wannan ayah za mu fahimci cewa shi yanka da sallah da sauran ayyukan addini Allah kawai ake yiwa,  ba a yinsu don wani kuma yinsu ga wani Allah shirka ne,  kamar yadda karshen ayar ya nuna. 


Acikin Hadisi kuma

 عن علي رضي الله عنه قال: حدثني رسول الله صلى الله عليه وسلم بأربع كلمات: «لعن الله من ذبح لغير الله، لعن الله من لعن والديه، لعن الله من آوى محدثا، لعن الله من غير منار الأرض» رواه مسلم


An kar6o daga Sayyidna Aliyyu Allah Ya kara yarda a gareshi,  ya ce "Manzon Allah 
صلى الله عليه وسلم
Ya gaya min wasu abubuwa guda hudu, ALLAH YA TSINEWA WANDA YAY YANKA DON WANIN ALLAH,  Allah Ya tsinewa wanda yake zagin iyayensa,  Allah Ya tsinewa wanda ya 6oye mai laifi, Allah Ya tsinewa wanda ya canja iyakar qasa. 

_Muslim ne ya ruwaito_.

A wannan Hadisi,  Manzon Allah 
صلى الله عليه وسلم
ya gaya mana qarara cewa,  duk wanda yay yanka don wanin Allah,  wato don Aljanu ko Rauhanay da dai sauransu,  to Allah Ya tsine masa. 

A wani Hadisin kuma

وعن طارق بن شهاب أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «دخل الجنة رجل في ذباب ودخل النار رجل في ذباب " قالوا: وكيف ذلك يا رسول الله؟ قال: " مر رجلان على قوم لهم صنم لا يجوزه أحد حتى يقرب له شيئا، فقالوا لأحدهما قرّب، قال: ليس عندي شيء أقرّب، قالوا له: قرّب ولو ذبابا، فقرّب ذبابا، فخلوا سبيله فدخل النار، وقالوا للآخر: قرّب، فقال: ما كنت لأقرب لأحد شيئا دون الله - عز وجل - فضربوا عنقه فدخل الجنة» رواه أحمد.

An kar6o da `Dariq bin Shihab,  ya ce "Manzon Allah 
صلى الله عليه وسلم 
Ya ce "Wani mutum ya shiga Aljanna saboda Quda🐝, wani kuma ya shiga wuta saboda Quda🐝. 

Sai suka ce "Ya Rasulallahi ya akay haka ta faru?"

Sai yace "Akwai wasu mutum biyu da suka zo wucewa ta wajen wasu masu bautar gunki,  a qa'idar masu bautar,  duk wanda zai wuce gunkin sai yayi masa yanka. Sai daya daga cikinsu yace "Ni bani da abinda zan yanka".  Sai suka ce,  
"To ko Quda ne ka yanka"
 Sai ya yanka Quda,  sai suka barshi ya wuce,  lokacin da ya mutu kuwa sai ya tafi wuta. 

Sai suka cewa dayan to kaima kayi yankan"
 Sai yace
 "Ai ba zan ta6a yin yanka don wanin Allah  Mai girma da daukaka ba". Sai suka sare masa kai,  sai kuwa ya shiga Aljannah". 

_Ahmad ne ya ruwaito wannan Hadisi_. 

Acikin wannan qissa,  Manzon Allah 
صلى الله عليه وسلم
ya gaya mana cewa, wani mutum ya yanka Quda saboda gunki,  amma da ya mutu sai Allah ya kaishi wuta. 
 Don haka,  duk wanda yay yanka saboda gunki ko saboda Aljani to in ya mutu wuta zai tafi. 

Karin bayani. 
Duk kankantar abinda Aljanu suka sa mutum ya yanka musu,  ko quda ne ko kiyashi ko qadangare ko kaza,  ko ma menene, to ya yi shirka kuma in ya mutu wuta zai tafi,  ba tsayawa. 

Wasu Aljanun basa hanawa a ambaci sunan Allah idan za ay yanka to amma dai wata hanya ce ta yaudara kuma shi ma shirka ne,  tunda dai don su aka yanka. 

Sannan wannan hukuncin yankan da muke magana,  ya shafi masu yin yanka don wani qabari,  ko a wata bishiya ko a wani bigire don girmama wani wanda shar'iar musulunci batay umarni da shi ba. 

Allah shi ne mafi sani.

SHIN AL-JANU SUNA BARIN JIKIN MUTUM IDAN YAY MUSU YANKA? 

Maganar gaskiya Aljanu basa barin jikin mutum idan yay musu yanka. 

Hasalima ga abubuwan da za su faru da kai bayan ka yi wa Aljanu yanka. 

1- Ka zama Mushriki, ka shiga cikin tsinuwar Allah kuma ka zama dan wuta,  kamar yadda ayoyi da hadisan da muka kawo suka tabbatar. 

2- Ka zama bawan Aljanu,  domin ka shiga cikin wadanda suke bautawa Aljanu ta hanyar yanka. 

3- Ka bayar da kanka,  Aljani ya raina ka.  Yanzu ya gane baka da wayo kuma kai jahili ne,  domin ya san shi mai laifi ne a wajenka amma kuma ga shi yana juya ka. 

4- Ka budewa kanka kofar da duk sanda Aljanin ya ji kwadayi zai zo wajenka,  ya ce ka yanka masa wata dabba ya sha jini. Don ba zai ta6a barinka ba,  tunda kanay masa abinda yake so. 

5- Aljanin zai tare a jikinka ko a gidanka kuma sai ya bibiyi `ya`yanka da jikokinka. Wannan tabbas ne. 

6- Yanzu ka rabu da Mala'iku masu nema maka gafarar Ubangiji,  kuma duk masu tsarki za suyi nesa da kai. 

Hmm,  wannan a takaice kenan.  Allah Ya kiyayemu. 

Amma duk wanda yasan ya ta6a yin yanka saboda neman lafiyarsa ko ta iyalansa to ya tuba kuma kada ya kara. Shi kenan,  Allah Zai yafe masa.


Sai Bashir Halilu ya ce. 
Mutane suna yi min korafin cewa rubutuna yana yin yawa,  basa iya karantawa har karshe. Ni kuma ina yin dogon rubutu ne don a samu fahimta sosai. Gaskiya akwai tarin hujjoji da kuma wasu bayanai da yawa da ya kamata ace na kawo,  to amma dole ne in takaita anan. 

Insha Allahu nan gaba kadan zan fara shirya seminar,  wacce masu Ruq'yah za su dinga halarta,  in gabatar nusu da paper kuma ay tambayoyi,  a amsa baki da baki. Har ma masu shawa'awa wadanda ba masu Ruq'yah ba za su iya halarta. 

Sannan don girman Allah masu yin _plashig_ ku dena,  duk wanda ya dauki lambata to ka bari sai kana da magana mai muhimmanci sannan kay kirana.  Duk wanda ya kara yi min plashing to zan yi blocking dinsa nan take,  insha Allah. 

Rubutuna na gaba zan yi shi ne akan HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MISULUNCI. In Allah Ya yarda. 

Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah,  masu yin Ruq'yah da harhada magungunan Musulunci.  
bashir.halilu@yahoo.com 
Lambar waya 08162600700, 08134434846.




Comments

Popular Posts