Posts

ALJANAR JARIRAI / ALJANU MASU SHIGA JIKIN KANANAN YARA

 AL-JANAR JARIRAI Aljana mai shiga jikin Qananan yara. Wasu suna kiranta Ummul Atfal أم الأطفال.  Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci 08162600700. A cigaba da kawo muku bayani akan Nau'ukan Aljanu da Rabe-rabensu da kuma irin cututtukan da suke sakawa mutane da hanyoyin magance su, yau insha Allahu za muy bayani ne a kan Ummul Atfaal, Aljana me shiga jikin Jariran mutane. Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya ce:  "Idan dare ya shiga ko kuma kun yamma ta, to ku kame kananan 'ya'yanku, domin awannan lokacin ne shaidanu suke yaduwa amma idan aka sami kimanin awa daya to kwa iya sakin yaranku. kuma idan zaku kwanta ku rufe kofofinku, idan zaku rufe ku ambaci sunan ALLAH. domin Shaidan ba ya iya bude kofar da aka rufe ta (da sunan Allah). Kuma ku kife qorukan ku. (jam'in QWARYA) Ku ambaci sunan ALLAH yayin da zaku kife. kuma ku rufe tukwanan ku, ku ambaci ALLAH lokacin da zaku rufe din, ko da wani abu ne ku dora a kai. ...

WALIYYAI DAGA JINSIN AL-JANU

WALIYYAI DAGA JINSIN AL-JANU. Acikin Aljanu akwai mutanen kirki, Waliyyai, Bayin Allah na gari kuma masoya Allah da ManzonSa. Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci http://bashirhalilu.blogspot.com Shiga cikin wannan shudin rubutun kayi downloading Application dinmu, wanda za ka dinga samun rubututtukanmu cikin sauki https://appsgeyser.io/7550770/Bashir%20Halilu% 20Tarbiyyah%20Islamiyyah Lambar waya 08162600700.        Kamar yadda mu ka san Addinin Musulunci wajen adalci, duk irin yadda wasu jama'a suke wajen aikata 6arna da fajirci, to indai suna da wani dan alkhairi ko yaya ne sai Allah Ya fade shi, koda kuwa sharrinsu ya fi yawa. Hatta giya da caca, sai da Allah Madaukakin sarki ya ce 'Acikinsu akwai cutarwa babba da kuma wani dan amfani kadan ga mutane'. Wato duk da su ba mutane ba ne kuma ba su da baki amma hakan ba ta sa saboda kyamar da Allah Yake yi mu su ya ki fadin cewa suna da amfani kadan ba. ...

ALJANU MASU SHIGAR MAI RUQIYYAH

AL-JANU MASU SHIGA JIKIN MASU RUQIYYAH DA KUMA MASU NAZARIN RAYUWAR AL-JANU. Jinnul jalab wat tahdheer. Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci http://bashirhalilu.blogspot.com. Lambar waya 08162600700. ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ. Ma'anar Jinnul Jalab Wattahdeer shi ne: wani nau'in Aljanu ne da suke kasancewa tare da mutum wanda yake da alaqa da su yana sani ko baya sani. Suna da taurin kai da saurin samun tasiri a jikin mutum. Mutum yana iya kirawo su a halin yana sani ko kuma ya gayyato su cikin rashin sani bisa kuskure. Da akwai hanyoyi da suke janyowa mutum Jinnul Jalab su kasance tare da shi, kamar: ★NEMAN DUNIYA Misali: Wadansu mutanen sukan nemi taimako a wajen bokaye idan za suy wani al'amari, su kuma bokayen sai su gaya musu wadansu abubu da za su aikata ko su karanta, idan sun yi haka sai Alja...

ASIRIN MALLAKA / YADDA AKE MALLAKE MUTUM TA HANYAR ASIRI

ASIRIN MALLAKA WATO ASSIHRUL MAHABBAH. Sihirin da ake yi domin a mallaki soyayyar mutum, a mallaki zuciyarsa kuma a dinga juya shi yadda ake so. Daga Cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci http://bashirhalilu.blogspot.com Lambar waya 08162600700. أعوذ بالله من الشيطان الرجيم بسم الله الرحمن الرحيم صلى الله على النبي الكريم Sihirin Mallaka ko Sihirin hada Soyayya, a Larabce ana kiransa da Sihrul Mahabbah السحر المحبة ko a ce Sihrut Tiwalah السحر الت...

HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MUSULUNCI

HUKUNCIN SHAN RUBUTU DA DAURA LAYA A ADDININ MUSULUNCI http://bashirhalilu.blogspot.com Menene matsayin daura Laya da shan Tofi da shan Rubutu a addinin Musulunci?. Daga shafin Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.    Abinda ya zo na Hadisan Manzon Allah صلى الله عليه وسلم game da yadda wasu mutane suke amfani da wasu abubuwa da sunan kare kansu daga wani sharri ko kuma janyowa kansu wani amfani. Inda mutane su kanyi amfani da Laya ko Qaho ko Wuri ko Zare ko Dutse, wasu kuma sukan yi Tofe-tofe ajikin wasu abubuwa ko a jikin mutum da sunan magani,  yayinda kuma wasu suke rubuta wadansu abubuwa su wanke,  su sha. Ko na Alqur'ani ko wanda ba na Alqur'ani ba. Da kuma matsayin yin wanka da ruwan Alqur'ani ko shafe jiki da shi. Da fari dai,  ga fadin Allah Madaukakin Sarki a cikin Suratuz Zumar:- بس...

YADDA AKE DAURE ALJANU A WATAN RAMADAN

YADDA AKE DAURE AL-JANU A CIKIN WATAN RAMADAN Me yasa Aljanu suke tashi ajikin mutane acikin watan Ramadhana,  bayan kuma an dauresu?. Daga cibiyar Sunnah Medicine http://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/   masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.  Lambar waya 08162600700. An kar6o Hadisi daga Aba Hurairata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ yace "Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻳﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ya ce "Idan watan Ramadan ya zo, se a bude kofofin Aljanna, a kulle kofofin wuta kuma A `DAURE SHAIDANU" Muslim ne ya ruwaito. ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰﺍﻟ...