YADDA AKE DAURE ALJANU A WATAN RAMADAN
YADDA AKE DAURE AL-JANU A CIKIN WATAN RAMADAN
Me yasa Aljanu suke tashi ajikin mutane acikin watan Ramadhana, bayan kuma an dauresu?.
Daga cibiyar Sunnah Medicine
http://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
masu yin
Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya
08162600700.
An kar6o Hadisi daga Aba Hurairata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
yace
"Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻳﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ya ce "Idan
watan Ramadan ya zo, se a bude kofofin Aljanna, a
kulle kofofin wuta kuma A `DAURE SHAIDANU"
Muslim ne ya ruwaito.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻩ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ( ﺇﺫﺍ ﺟﺎﺀ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻓُﺘّﺤـﺖ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻨﺔ،
ﻭﻏُـﻠّـﻘـﺖ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻨﺎﺭ، ﻭﺻُﻔّـﺪﺕ ﺍﻟﺸـﻴﺎﻃﻴﻦ )
ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
Ana daure Shaidanu a cikin watan Ramadan, kamar
yadda Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ عليه ﻭﺳﻠﻢ
ya sanar da mu.
To amma wadansu mutanen sukance wasu-wasu
yana yi musu yawa a cikin watan Ramadan da
rashin son yin ibada.
Haka ma wasu masu lalurar ta Aljanu ba sa
denawa a cikin watan Ramadan har ta kan kai ma
Aljanun suna bayyana a jikinsu ko kuma su fito
musu a fili, duk kuwa da cewa mun yi imani lallai
an daure su.
Duk mai yin rukiyyah ko mai ba da maganin Aljanu
ya san lallai Aljanu suna tashi cikin wayan Azumin
Ramadana kuma suna damun mutane.
Wasu Malaman musulunci, (kafin mu kawo maganganun na su) suna cewa
"Ai shaidanu ake
daurewa ba Aljanu ba".
Amma kuma wani hadisin yana nuna mana cewa
Shaidanu suna nan a watan Ramadana, har ma
suna iya saka wasuwasi a zuciyar mutane.
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺤﻪ ﻋﻦ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ
ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ : ﺇﻥ ﺻﻔﻴﺔ ﺯﻭﺝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺃﺧﺒﺮﺗﻪ ﺃﻧﻬﺎ ﺟﺎﺀﺕ ﺇﻟﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺗﺰﻭﺭﻩ ﻓﻲ ﺍﻋﺘﻜﺎﻓﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﺸﺮ ﺍﻷﻭﺍﺧﺮ
ﻣﻦ ﺭﻣﻀﺎﻥ، ﻓﺘﺤﺪﺛﺖ ﻋﻨﺪﻩ ﺳﺎﻋﺔ، ﺛﻢ ﻗﺎﻣﺖ ﺗﻨﻘﻠﺐ ﻓﻘﺎﻡ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻌﻬﺎ ﻳﻘﻠﺒﻬﺎ، ﺣﺘﻰ ﺇﺫﺍ ﺑﻠﻐﺖ
ﺑﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻋﻨﺪ ﺑﺎﺏ ﺃﻡ ﺳﻠﻤﺔ ﻣﺮ ﺭﺟﻼﻥ ﻣﻦ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
ﻓﺴﻠﻤﺎ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻬﻤﺎ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻠﻜﻤﺎ، ﺇﻧﻬﺎ ﺻﻔﻴﺔ ﺑﻨﺖ
ﺣﻴﻲ، ﻓﻘﺎﻻ : ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻛﺒﺮ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ، ﻓﻘﺎﻝ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﺇﻥ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻳﺒﻠﻎ ﻣﻦ ﺍﺑﻦ ﺁﺩﻡ
ﻣﺒﻠﻎ ﺍﻟﺪﻡ، ﻭﺇﻧﻲ ﺧﺸﻴﺖ ﺃﻥ ﻳﻘﺬﻑ ﻓﻲ ﻗﻠﻮﺑﻜﻤﺎ ﺷﻴﺌﺎً
Wannan hadisi da Bukhari ya ruwaito, yana bamu
labarin cewa, watarana Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ
yana i'itikafi a goman karshe na watan
Ramadana, se matarsa Safiyya ta kai masa ziyara a
masallaci.
Lokacin da za ta tafi sai Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ya rako ta bakin kofar Masallaci. Sai ga
wasu mutane sun zo wucewa, sukaywa Manzon
Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻲ ﻭﺳﻠﻢ sallama.
Sai Annabi ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kira su yace musu
"Wannan mata
ta ce Safiyyah" (don kar su zaci wani abu a ransu)
Sai suka ce "Sub'hanAllahi". (Maganar tay musu
nauyi).
Sai Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya ce
"Ai Shaidan yana shiga duk inda jini yake shiga a jikin
mutum, to shi ne nake gudun kada ya jefa wani
abin a zuciyarku"
Daga wannan kissa za mu fahimci cewa a cikin
goman karshe na Ramadan kwanakin da suka fi
kowanne falala amma Shaidan zai iya sakawa
mutum wasuwasi, har Manzon Allah
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ عليه وسلم
da kansa yana gayawa Sahabban sa cewa yana tsoron kada Shaidan ya jefa wani abu a cikin zuciyarsu,
duk kuwa da cewa an daure Shaidanun.
To amma wane irin dauri ake yi wa Shaidanun ne?,
kuma su kadai ake daurewa ko harda Aljanu?
sannan akwai ma bambanci tsakanin Aljanu da
Shaidanu?
Mallam Albajiy ﺍﻟﺒﺎﺟﻲ
a cikin sharhin Muwadda'i
ﻣﻮﻃﺈ
ya yi dogon bayani akan wannan mas'ala
kuma yace
"Abinda ake nufi da daure Shaidanu shi
ne za su zama kamar daurarru ne saboda aikinsu
ba shi da wani tasiri. Domin dukkan ayyukan da
suke sakawa ayi na sa6o Allah yana yafesu a cikin
wannan watan, don haka ba su da wani tasiri. Da
su da daurarru duk daya ne.
Alhafiz bin Hajaril-Athqalaniy ya fada a cikin
Fat'hul Bariy cewa
"Abinda ake nufi da daure
Shaidanu a watan Ramadana, ana nufin Aljanu
masu hawa sama domin su sato maganar
Mala'iku. To su ake daurewa, domin kada su saci
maganar da ake saukarwa ta Alqur'ani, don kuwa a
watan Ramadana ake saukar da shi"
Ya ce "Kuma ana daure su ne iya cikin dare na
Ramadan banda rana.
*
*
Maganganun da Malami sukay akan wannan
mas'ala suna da yawa amma a takaice dai
1- Akwai masu Ganin cewa lallai Shaidanun ake
kamawa a daddaure su da ankwa dauri na hakika
sannan in Ramadana ya wuce a kwance su.
2- Wasu Malaman suka ce, e dauri na hakika ake
yi wa Shaidanun, amma ba dukkansu ba, manyan
kawai ake daurewa masu dagawa sosai.
3- Wasu Malaman suka ce "Aljanu masu zuwa
sama don su sato maganar Mala'iku su ake
daurewa amma sauran suna nan.
4- Wasu Malaman suka ce Daure Shaidanu yana
nufin a hana su tasiri. Ta yadda ba za su iya saka
mutane aikata sa6o kamar yadda suke yi a sauran
watanni ba.
5- Yayainda a fahimtar wasu Malan kuma shi ne,
duk sa6on da Shaidan ya saka musulmi ya aikata,
to indai ya tuba Allah zai saurin yafe masa don
kuwa wata ne na afuwa da gafarar zunubai.
Allah shi ne ya fi sanin wannene daidai.
Amma dai lallai Shaidanu tasirinsu na raguwa a
cikin watan Ramadan domin kuwa
i) Wadanda ba sa iya fita sallar Asuba, to idan
Ramadan ya zo za ka suna zuwa masallaci.
ii) Wadanda ba sa sallah a jam'i ko kuma akan
lokaci, to cikin Ramadana za ka ga suna kulawa
sosai.
iii) Gidajen aikata badala musamman wadanda
yayan musulmai suke dan lekawa, ana rufesu ko
kuma 6arnar tana raguwa sosai.
iv) Bokaye da yan bori da sauran masu aiki da
Shaidanu, idan watan Ramadana ya zo suna yin
sallama da Shaidanunsu, abinda suke kira 'Rakiyar
wata' kuma ba sa aikinsu cikin watan.
Da dai alamomi da yawa dake nuna cewa lallai
Shaidan da danginsa ba su datasiri a cikin wannan
watan.
Don haka fahimtar da mu ka fi dauka ita ce Kodai
daure Shaidanu yana nufin a daure wasu daga
cikinsu ne ko kuma yana nufin ana rage musu
tasiri ne.
Domin muna yin Rukiyya a cikin Azumin
Ramadana kuma muna kama Aljanun a jikin
mutane, saidai yawancin Aljanun da suke shafar
mutane a cikin watan Ramadana musulmai ne. Domin ko ayau dinnan 5/Ramadhan, 1439, ni Bashir, na yiwa wata mata rukiyyah, kuma na yi magana da Aljana ajikinta.
Wallahu A'alamu.
Daga shafin Bashir Halilu Tabiyyah Islamiyyah. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
YADDA ZA KA GANE KANA DA ALJANU KO
KUMA AN YI MA KA SIHIRI
Ana gane mai Aljanu ne ko wanda aka yiwa
sihiri ta hanyoyi guda uku:
1) Alamomin boye.
2) Alamomin sirri.
3) Alamomin zahiri.
.
.
*Alamomin boye sune alamomin da shi mara
lafiyar
ne kawai ya ke iya ji ko ganin su a tare da
shi.
Kamar
*Yawan mafarki mai abin tsoro.
*Yawan ciwon kai dab da magriba.
*Jin abu nai ma yawo a jiki kamar kiyashi.
*Haka kawai gaban mutum ya dinga faduwa.
*yawan mafarkin saduwa.
*Rashin son yin aure.
*Bacin rai mara dalili.
*Yawan tunane_tunane marasa amfani.
*Gane-ganen abubuwan tsoro kamar karnuka,
macizai, kuraye da dai sauran su.
*Jin kasala lokacin da za ka yi sallah.
*Jin ciwon kai lokacin da ake karanta
Alqur‘ani.
*Rashin fahimtar karatu ko kuma saurin
zubewar sa,
musamman ma na addini.
*yawan jin an kira sunan ka kuma ka waiwaya
ba ka
ga kowa ba.
*yawan jin kamar an caka ma ka kibiya ko
allura a
jiki.
*za ka kwanta barci da wuri amma ya ki
daukar ka
sai dab da asuba.
*Yawan batan kudi ko kayan amfani.
*Yawan fada ko gaba da mutane.
Da dai sauran alamomi.
Ya a ke gane mai Aljanu? ko wanda aka jefe
shi da Sihiri(kashi na biyu)
Ana gane mai Aljanu ne ta hanyoyi guda uku
kamar
yadda mu ka fada tun a farko
1) Alamomin 6oye
2) Alamomin sirri
3) Alamomin zahiri
Mun yi bayanin alamomin 6oye, yanzu ga
alamomin
sirri.
Alamomin sirri alamomi ne wadanda se
wanda ke
tare da mara lafiyar ko da yaushe shi ne zai
dinga
ganin su ko fuskantar su.
* Mutum ya dinga magana a lokacin da ya ke
bacci.
* Nauyin Bacci mara misali.
* Dadewa a bandaki alhali ba abin da mutum
ya ke
yi.
* saurin fushi.
*Son zama a duhu.
*Son zama a waje mai kazanta.
*Zama da kazanta da rashin son yin wanka.
*Surutu barkatai.
*Rashin dariya ko murmushi sanda a ke abin
dariya.
*Rashin son yin sallah.
*Yawan harare-harare.
*Kura wa mutane ido.
*Yawan dariya ko murmushi ba dalili.
*Taurin kai.
*Rashin samari ga Budrwa.
Da dai alamomi da yawa.
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yi ruqiyyah da harhada magunguna na Musulunci. Shiga shafunmu na facebook acikin wannan shudin rubutun, sai ka danna like
http://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya, 08162600700.
Comments
Post a Comment