ALJANU MASU SHIGAR MAI RUQIYYAH
AL-JANU MASU SHIGA JIKIN MASU RUQIYYAH DA KUMA MASU NAZARIN RAYUWAR AL-JANU. Jinnul jalab wat tahdheer. Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci http://bashirhalilu.blogspot.com. Lambar waya 08162600700. ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ. Ma'anar Jinnul Jalab Wattahdeer shi ne: wani nau'in Aljanu ne da suke kasancewa tare da mutum wanda yake da alaqa da su yana sani ko baya sani. Suna da taurin kai da saurin samun tasiri a jikin mutum. Mutum yana iya kirawo su a halin yana sani ko kuma ya gayyato su cikin rashin sani bisa kuskure. Da akwai hanyoyi da suke janyowa mutum Jinnul Jalab su kasance tare da shi, kamar: ★NEMAN DUNIYA Misali: Wadansu mutanen sukan nemi taimako a wajen bokaye idan za suy wani al'amari, su kuma bokayen sai su gaya musu wadansu abubu da za su aikata ko su karanta, idan sun yi haka sai Alja...