NAU'O'IN ASIRAI GUDA BIYU DA YADDA AKE WARWARE SU
NAU'IN ASIRAI GUDA BIYU DA KUMA YADDA AKE WARWARESU.
Asirin da aka saka a jikin mutum da kuma wanda aka binne a wani waje daban.
Wato Assihrul Ma'akul da kuma Assihrul Madfun.
1) ASSIHRUL MA'AKUWL
Wato Sihirin da mutum ya ci ko ya sha ko wanda Aljanu su ka yi masa ajjiya acikin jikinsa.
Daga Shafin Sunna Medicine, Masu Yin Ruqiyyah Da Harhada Magunguna na Musulunci.
Shiga shafinmu na facebook acikin wannan shudin rubutun, sai ka danna like
https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700.
As sihrul Ma'akuwl ko kuma Sihrul Mashruwb, daya ne daga cikin nau'o'in Sihiri da akan iya yiwa mutum don a cutar da lafiyar jikinsa ko a 6ata masa tunani.
Saidai shi Sihrul Ma'akul ana yin sa ne ta hanyar zubawa mutum wani abu a cikin abinci ko abin sha; idan ya ci ko ya sha sai sihirin ya kama shi.
Misali, ana iya hada wata guba ta tsafi, sai a zuba a cikin abincin mutum ko ruwan shansa ko ruwan wankansa ko ay masa hayaqi da shi ko a zuba a cikin turare. To matukar mutum yay amfani da abun ko ya shaqi warinsa, shikenan, sihirin ya kama shi.
A mafi yawan lokaci ma, Aljani ake baiwa maganin ya zubawa mutum a abincin ko kuma ya kwarara masa a jikinsa. Aljani ya kan ma shiga kai tsaye zuwa cikin mutum ko sauran jikinsa domin sanya masa guba ko sihiri.
Sihrul Ma'akul, mafi yawanci ana yinsa don a sanyawa mutum rashin lafiya. Hakama idan ana so a mallaki zuciyar wani yawanci ana zuba masa wani abu ne a abinci ko abinsha ko ta hanyar jin kamshi.
Wannan nau'in sihiri wato Sihrul Ma'akuwli, yana da saurin tasiri a jikin mutum nan da nan amma ta wani bangaren kuma ya fi Sihrul Madfuwn saukin magani.
Misali, idan akaywa mutum Sihrul Ma'akuli don a kashe shi, to yana cin abincin a take zai mutu. Haka ma idan akay masa don ya haukace ko ya samu rashin lafiya ko don a mallaki zuciyarsa, to yana yin amfani da abun nan take ciwon zai same shi ba 6ata lokaci.
Saidai sihirin ya kan samu rauni ko rashin tasiri da zarar mutum ya yi amai bayan ya ci ko ya sha.
WASU DAGA CIKIN ALAMOMIN SIHRUL MA'AKUWL.
١- Tashin Farko mutum zai fara gamuwa da ciwon ciki mai tsanani bayan ya ci sihirin ko kuma ya sha.
٢- Mutum zai dinga yin amai me wari kuma jajawur, saidai wannan ba koda yaushe yake faruwa ba.
٣- Idan aka baiwa mutum ruwan addu'a ko ya sha zuma ko kuma kowane irin maganin sihiri, to zai ji cikinsa yana murdawa ko kuma yay amai.
٤- Idan ana yi wa mutum karatun Rukiyyah sai ya dinga kakari ko kuma yay amai kuma za a ga amain yana motsi kamar wasu abubuwa ne a ciki, alamar ya amayar da sihirin kenan.
٥- Idan ana karantawa mutum Ruqiyyah za a ji cikinsa yana kara wani kuma yana shaquwa ko tusa.
٦- Idan ana yi wa mutum Rukiyyah, cikinsa da kuma sauran jikinsa gaba daya suna daukar zafi. Shi ma alama ce ta cewa ya ci sihiri ko kuma ya sha.
٧- Fitowar wari mara dadi daga bakin mutum kuma lokacin da ake masa Rukiyyah za a ji yana karuwa.
٨- Mutum zai dinga jin kamar ana jan 'ya'yan cikinsa, lokacin da ake masa karatu kuma zai dinga jin yana karuwa.
٩- Haka kawai mutum zai dinga jin rashin son cin abinci wani lokacin. Wani kuma cin abincin ne yake masa yawa.
١٠- Raunin gani. Wato ya zama mutum ba ya gani sosai, wani ma za ka ga kwantsa na yawan fita daga idonsa.
١١- Mutum zai dinga ganin abubuwan tsoro kuma koda ya rufe idonsa sai ya gansu.
١٢- Duk inda aka ta6a a jikin mutum zai dinga jin zafi, musamman ma inda sihirin ya fi yawa a jikinsa.
١٣- Mafi yawa numfashi ya naywa wanda aka yi wa Suhrul Ma'akuli wahala, wani kuma yana fama da gurnani lokacin bacci.
١٤- Wanda akaywa Sihrul Ma'akuli idan anay masa Ruqiyyah za a ga fuskarsa tay baqi, idan aka gama kuma sai fuskar ta washe.
١٥- Idan ana cikin Ruqiyyah mutum zai ce yana jin fitsari. Wani se yay fitsari sau biyar a rabin awa, a lokacin da ake masa karatun Ruqiyyah. Wani ma zai iya yi a zaune.
١٦- Lokacin da akewa mutum Ruqiyya zai dinga ganin haske, kamar walqiya, yana gifta shi. Wannan alama ce ta cewa Aljaninsa ya qone ko sihirin ya fita daga jikinsa.
١٧- Idan ana Ruqiyyah za ka ji mutum yana yin tusa ko riyhi, to wannan yana nuna ya ci ko ya sha sihiri sannan sihirin yana fita daga jikinsa ta hanyar tusar.
١٨- Za ka dinga mafarki wani ya ka wani abu mara dadi kana sha ko kana ci. Musamman za ka dinga mafarkin wani ya miko maka danyen nama kana ci, kodai wani abu daban.
١٩- Mutum zai dinga mafarki kamar wani mutum ya kama shi ya saka masa wani abu a cikinsa ko bakinsa ko mace tay mafarkin an saka mata wani a gabanta.
٢٠- Zubar jini mara tsayawa ga mace ko namiji.
21- Yawan ciwon ciki mai tsanani kuma idan an je asibiti za a ce ba a ga komai ba.
22- Musamman mace, za ta dinga ji abu nay mata yawo acikinta zuwa mararta kuma za a ce an kasa gane ko menene.
Da dai alamomi da yawa.
☆ Abinda yasa muke yawan ambaton Ruqiyyah a cikin wanan bayani na Sihrul Ma'akuli shi ne, kamar yadda mukay bayani Sihri ne mai hadarin gaske da saurin tasiri a jikin mutum.
Indai akaywa mutum da wahala ya kai minti daya bai fara aiki a jikinsa ba. In ma an yi masa ne don a kashe shi to zai iya mutuwa a take. Haka idan an yi masa ne don ya haukace to zai iya haukacewa a take a wajen.
Ba wani abu da zai iya samun mutum saida iznin Allah. Don haka wani mutumin sihrin zai dade a jikinsa yana wahalar da shi kafin ya hallaka shi ko kuma yay masa abunda aka nufa.
Shi yasa yana da kyau duk wanda ake zaton an yi masa Sihrul Ma'akuli to ay masa Ruqiyya ba tare da bata lokaci ba. Saidai yana da kyau mai Ruqiyyah ya sani, a irin wannan Sihrin Aljani ba magana yake ba, saidai aga alamomin da muka ambata a baya.
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Shiga shafinmu na facebook acikin wannan shudin rubutun, sai ka danna like
https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700.
2)ASSIHRUL MADFUWN
ﺍﻟﺴﺤﺮ ﺍﻟﻤﺪﻓﻮﻥ
Wato Sihirin Da Aka Binnewa Mutum
.
.
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.
Shiga shafinmu na facebook acikin wannan shudin rubutun, sai ka danna like
https://www.facebook.com/sunnahmedicinepage/
Lambar waya 08162600700.
Abinda ake nufi da Sihrul Madfuni shi ne : Nau'in Sihirin da aka hada wasu abubuwan tsafi kamar layoyi ko wani abu, aka je wani waje aka binne don a cutarda wani mutum.
Irin wannan sihiri akan hada da sunan mutum ko wani 6angare na tufafinsa ko qasar sawun kafar mutum ko gashin kansa ko farcensa da dai sauransu; sai a je a binne a inda Aljanu suka bada umarni kamar bola ko masai ko tsohuwar rijiya ko cikin kabari ko gidan tururuwa da dai sauransu.
Irin wannan sihiri yana da matukar hadari da saurin tasiri da kuma tsananin cutar da wanda aka yi wa shi.
.
Irin wannan Sihiri galibi shi ne mutum zai ta bin hanyoyin karya Asiri kala-kala amma ya ga tamkar ba ya yin komai ko kuma yay ta shan magani amma ya ga ba wani canji.
Koda a wajen masu Ruqiyyah da masu magunguna, Sihrul Madfuwni, wato sihrin da aka binne yana da matukar wahalar magani da wuyar gane kansa sama da Sihrul Ma'akuwli ﺳﺤﺮ ﺍﻟﻤﺄﻛﻮﻝ
wato Sihrin da aka sakawa mutum a abinci ko Sihril Maqruw'i ﺳﺤﺮ ﺍﻟﻤﻘﺮﺅ ،
wato Sihrin da akaywa mutum ta hanyar karanta dalasiman bokanci dadai sauransu.
Dalili shi ne: shi irin wannan Sihirin kamar wani Generator ne ake kunnowa daga wani waje ya dinga baiwa jikinka wuta. To matukar ba a kashe generatorn ba wuta ba zata dena zuwa jikinka ba komai kariyar da zaka baiwa jikin naka. Koda zaka yanke wayarin din to Aljanu zasu sake hada shi. Don haka mafita kawai a kashe wannan generatorn mai bada power.
Abin misali ne irin yadda akaywa Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Sihrul Madfuwni da kuma irin yadda ya cutar da shi.
.
Wannan kissa sananniya ce kuma mun dade da kawota a wannan shafi na Sunnah Medicine, inda wani Bayahude ya samo gashin kan Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
da matajin kansa, ya hada da hudar dabino da sauran kayan tsafi, yay masa Sihiri, ya binne a cikin tsohuwar rijiya.
To irin wannan Sihiri da ake hadawa da wasu abubuwa na mutum a je a binne a wani waje shi ake kira Sihrul Madfun.
Lokacin da akaywa Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
irin wannan Sihiri sai da Mala'ika Jibrilu ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ya gaya masa wajen da aka binne sihirin, shi kuma Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ya tura aka je rijiyar aka haqo masa sihirin ya warware shi da hannunsa sannan ya samu lafiya.
Wannan dalili ne yasa yawancin masu magani suke da akidar cewa indai akaywa mutum Sihrul Madfuni to dole sai an binciko inda sihirin yake an je an haqe sannan mutum zai samu lafiya.
To saidai za ka iya gane cewa an yi wa mutum sihiri tun daga kallon yanayinsa, sannan zaka iya gane nau'in sihirin da akay masa daga bayanansa amma abu ne mai matukar wahala ka gane cewa a waje kaza, a gari kaza ko a qasa kaza aka binne sihirin balle ka je ka ciro shi.
Sannan wani Sihirin Aljanu ake baiwa su je su binne shi a karkashin teku ko wani waje mai hadari inda Dan-Adam ba zai iya zuwa ba, kai hatta wani Aljanin bai isa ya doshi wajen ba.
Don haka indai aka ce sai an ciro shi sannan mutum zai samu lafiya to gaskiya an dauko babban aiki mara sauqi.
Muna bin hanyoyi guda biyu ne don warware irin wannan sihirin.
1) Hanya ta farko ita ce: Shi Aljanin da aka hada kai da shi aka yi wa mutumin Sihiri sai mu kamo shi mu tambaye shi a inda Sihirin yake. Idan ya fada sai mu ce ya je ya cire.
Idan kuma Aljanin ba zai iya cirewa ba, sai mu ce ya gaya mana wajen mu mu je mu cire.
Idan wajen ya yi nisa kamar wata qasa ko wani waje mai wahala kamar qasan teku da dai sauransu, sai a sa 'yan uwansa su taimaka masa ya cire, bisa sharadin in ba su cire ba za a kashe shi.
2) Hanya ta biyu ita ce : wani lokacin shi kansa Aljanin da aka hada Sihrin da shi bai san inda bokan ya binne ba. Ko kuma ya kasance Aljanin ya qi kamuwa kwata-kwata ko kuma an yi alkawari zai cire amma sai ya gudu, ya ki cirewa, to wannan saidai ayi ta addu'a da shan magunguna.
Idan ku ka duba wannan hoton da ke kasa, za ku ga yadda aka binne layoyi acikin karkashin kasa da yadda Aljanu su ka kewaye layar da yadda dafin sihiri yake tasowa daga jikin layoyin da kuma yadda yake mamaye jikin mutum.
Wannan dafin da layoyin ke fitarwa, shi yake riskar mutum duk inda yake kuma ta cikinsa Aljanun su ke bi suna shiga jikin mutum. Shi yasa wanda akayiwa Sihrul Madfun ake shan bakar wahala kafin a kama Aljaninsa, domin da an ta6a shi sai Aljanun su bi ta cikin wannan dafin, su koma jikin layoyin, su la6e.
Cire Sihrul Madfun yana da matukar hadari ga mutum, saboda wasu layoyin akwai Aljanu aciki, don haka matukar mutum ya ta6a to za su iya haukata shi ko su sa masa rashin lafiya. Don haka a shawarce, kada mutum yay karambanin bude laya idan ya tsinta, saidai kawai ya je ya konata a hakanta kuma ba a konawa acikin gida ko inda hayakin zai dinga dawowa mutane suna shaka. In kuma mutum yana so lallai sai ya bude to ya tabbatar ya yi addu'a yayin budewa, kamar yadda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya karanta Falaqi da Nasi, yayin warware sihirin da aka yi masa.
Allah Ya tsare mu daga sharrin azzulamai da dukkan macuta.
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.
Shiga shafinmu na Youtube domin kallon bidiyo na abubuwan da muke kawowa
https://youtube.com/channel/UCw1NWWsxJJbQkXcqHA127GA
Lambar waya 08162600700.
Comments
Post a Comment