AMFANIN ZAITUN
AMFANIN ZAITUN GA DAN'ADAM
Daga shafin Magunguna a Musulunci.
https://www.facebook.com/groups/842715785785303/
Lambar waya 08162600700.
Amfanin zaitun a jikin ɗan Adam wanda ya kamata mu sani, Shi dai zaitun itaciya ce mai albarka da kuma ba da cikakkiyar lafiya a jikin ɗan Adam, kamar yadda muka sani cewa, zaitun abu ne mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninsa a cikin ALKUR’ANI MAI GIRMA
haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W)
An karɓo daga sayyadina Umar yana cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce ku yi abinci da man zaitun kuma ku shafa shi a jikinku, domin haƙiƙa shi yana daga a cikin bishiya mai albarka. tirmizi ne ya rawaito
Daga Cikin aikin da man zaitun yake a jiki
CIWON CIKI
Duk mutumin da yake ciwon ciki, sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali, ya hada da garin habbatussauda ya cakuɗa, ya sha safe da yamma. Ya samu kamar sati ɗaya yana sha ko kina sha, insha Allah zai samu lafiya.
CIWON KAI
Duk mutumin da yake ciwon kai, to sai ya samu man zaitun, yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali ɗaya da safe da rana da dare, insha Allah zai samu lafiya.
CIWON HAKORI
Duk mutumin da yake ciwon haƙori, sai ya samo ganyen zaitun da ‘ya’yan habbatussauda, ya saka su a cikin garwashi, ya buɗa bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.
CIWON HANTA
Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo, sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali ɗaya da safe ɗaya da rana ɗaya da dare.
CIWON DADASHI
Duk mutumin da yake ciwon dasashi, sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.
CIWON SUKARI
Duk wanda ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana haɗawa yana sha, kafin ya kwanta barci insha Allah
CIWON ASMA
Duk mutumin da wannan ciwon ya kama shi, to sai ya samu ganyen zaitun ko ‘ya’yansa ya dinga turarawa.
CIWON KODA
Duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana. insha Allah.
CIWON BAYA
Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaɓa ya dinga shafawa a bayan insha Allah.
CIWON RAMA
Duk mutumin da ya ga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zai yi ƙiba.
ZAZZAƁI MAI ZAFI
Duk mutumin da ya kamu da zazzabi mai zafi, to sai ya dinga shan man zaitun cokali ɗaya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa a ciki, yana shafe jikinsa da shi insha Allah.
KARFIN MAZAKUTA
Duk mutumin da ya samu kansa a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa a cikin ruwan ɗanyan ƙwai, sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum insha Allah zai samu ƙarfin mazakuta sosai.
Kada ka gaji duk wani magani da ka gani ka gwada za ka dace insha Allah.
KYAWUN FUSKA
Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, ta yi fari, wanda ba zai cutar da shi ba, to, ya dinga shafa man zaitun da na habbatussauda, in zai kwanta barci, bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo, zai yi mamakin yadda fuskarsa za ta koma.
ZUBEWAR GASHI.
Duk matar da gashinta ba ya fitowa sosai, ko in ya fito sai ya zube, to sai ta samu ruwan zafi, ta wanke kanta da shi, sannan bayan ya ɗan bushe, sai ta zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kanta da shi gaba daya kullum.
ƘARANCIN JINI
Duk mutumin da yake da ƙarancin jini a jikinsa, to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a rana.
BASIR
Duk mutumin da yake shan wahala in ya zo zai yi bayan gida, wani ma sai ya yi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaɓa sai ya tura shi a cikin duburarsa.
CIWON MARA GA MATA
Duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara, saboda fitar jini, in tana so ta samu sauƘin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana haɗawa da ruwan tsamiya tana sha, insha Allah duk lokacin da za ta yi haila ba zai mata ciwo ba.
SANYIN ƘASHI
Duk wanda ƙashinsa ya yi sanyi, ba ya iya motsa shi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha, yana kuma shafawa a wajen insha Allah.
Comments
Post a Comment