ALJANU MASU SHIGAR MAI RUQIYYAH

AL-JANU MASU SHIGA JIKIN MASU RUQIYYAH DA KUMA MASU NAZARIN RAYUWAR AL-JANU.

Jinnul jalab wat tahdheer.

Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na Musulunci http://bashirhalilu.blogspot.com.
Lambar waya 08162600700.

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ.

Ma'anar Jinnul Jalab Wattahdeer shi ne: wani nau'in Aljanu ne da suke kasancewa tare da mutum wanda yake da alaqa da su yana sani ko baya sani.
Suna da taurin kai da saurin samun tasiri a jikin mutum.
Mutum yana iya kirawo su a halin yana sani ko kuma ya gayyato su cikin rashin sani bisa kuskure.

Da akwai hanyoyi da suke janyowa mutum Jinnul Jalab su kasance tare da shi, kamar:

★NEMAN DUNIYA
Misali: Wadansu mutanen sukan nemi taimako a wajen bokaye idan za suy wani al'amari, su kuma bokayen sai su gaya musu wadansu abubu da za su aikata ko su karanta, idan sun yi haka sai Aljanu su shiga jikinsu su dinga taimaka musu.
Wanda ya samu Aljani ta wannan hanya a karshe Aljanun suna saka masa ciwon hauka da tsoro.
Ta yadda zai kasance ba wanda yake tsoro kamar Aljani kuma su za su dinga gaya masa abinda zai yi da rayuwarsa.

★NEMAN KUSANCI DA AL-JANU.
Wato mutum kai tsaye ya nemi wata hanya da ake Mallakar Aljani ko Rauhani.
Ta hanyar aikata musu wani abu da suke bukata kamar wuridi kuma su yanka masa albashin da zai dinga biyansu a duk sati ko wata ko kuma shekara-shekara.
Albashin ya kan kasance kudi ne ko kuma wata dabba zai dinga yanka musu ko ya dinga ba su giya dadai sauransu.
Mafi yawan masu bin wannan hanya su ne bokaye. Wadanda sukewa mutane aikin mugunta kuma galibi sun fi yin amfani da sarakunan Aljanu da kuma manyan arnaku jikin Aljanu.
Wanda ya samu Aljani ta wannan hanyar sukansa ya zama mara imani, makaryaci kuma mara son ibada.
Aljanu suna sakawa bokaye wasu cututtukan sama da guda goma. Na yi bayaninsu a cikin posting dina mai taken SIFFOFIN BOKAYE. mai bukata zai iya dubawa a shafina na facebook ko gmail.

★ JINNUL JALAB BISA KUSKURE
Mutum ya kan iya janyowa kansa Jinnul Jalab a bisa kuskure.
Misali
1) Mutum ya ji ana wata waqa kamar ta indiya ko ta maguzawan turai, bai san abinda ake fada ba, ashe kirari akewa Aljanu.
To in mutum ya dinga rera waqar su kuma Aljanun za su zo su shiga jikinsa don sun ji ana kiransu.

2) Yin wata alama ta bautar Shaidan. Kamar yin wani nau'in salo idan za a dauki hoto ko murna idan an ci ball.
Kamar mutum yay rawar DAB ko kuma mutum ya banqare kiji ya wara hannuwansa idan ya ci ball domin alama ce ta masu bautar jemage.
Ko kuma mutum yasa hannu ya rufe ido daya idan zai dauki hoto domin alama ce ta masu bautar Shaidan mai ido daya (one eye devil) da dai sauransu.
Hatta a masu waqoqin Hausa akwai masu waqar bautan Shaidan. A mafi yawan yan bori masu Garaya suna yi.
Haka ma misalin waqoqin Sa'adu Bori na Nijar. Kamar waqarsa mai taken "Mai dawa ka cece ni"
Za ka ji mutane suna yin wakar kuma ana saka ta a gidajen rediyo.

3) Wasu mutanen kuma sukan yi kuskure su gayyatowa kansu Aljanu ba tare da sun sani ba ta hanyar karanta littattafan `Dibbu wadanda ke dauke da bayanin yadda ake kiran Alajni daki-daki.
A wannan halin da suke karanta wadannan kalmomi a matsayin suna nazari, to a daidai lokacin su kuma Aljanu za su kusanto su ne domin sun ji ana yi musu kirari, har sai su shiga jikin mutum ba tare da ya sani ba.
4) Wasu mutanen in ba su da lafiya sukan yi laya su daura a kansu ko su rataya a wuyansu.
Wata layar sunayen Rauhanan Aljanu ko Shaidanun Aljanu kawai ake rubutawa a cikinta. To idan mutum ya maqala a jikinsa ko a gidansa ko kantinsa, Aljanu za su zo ne su zauna tare da shi ba tare da ya sani ba.
Wanda Jinnul Jalab suka shafe shi ta wannan hanyar suna sa hi ya zama duk lokacin da bai amfani wannan layar ba to zai ji ba shi da lafiya ko kuma ya dinga jin ba zai samu sa'a ba.

★JINNUL JALAB BISA GANGANCI
Akwai mutane masu karambani misali mutum ya ce " Bari ya je wajen garaya ya ga yadda Aljanu suke rawa ko yadda suke wasa da wuta.
Ko kuma mutum ya dinga kutsa kai a guraren da ake cewa akwai Alajnu ya ce bari ya je ya gani.
To irin wannan ma akan samu Jinnul Jalab su shafe shi. Mafi yawa kuma sun fi sakawa mutum rashin lafiya da mafarkin mutuwa.

★ JINNUL JALAB TA HANYAR TAIMAKO
Da akwai wadanda taimako yakan kai su su samu Aljnu a jikinsu.
Kamar wata yarinya ta tada Aljanu a jikinta, mutum ya zo yana kokarin cire mata su. Ko kuma Aljanu su takurawa wani gida mutum ya je kai agaji.
To ta wannan hanyar ma na iya samu Jinnul Jalab su shafi mutum.
Amma shi wannan abinda ake bukata shi ne ya zamanto mutum ya iya karatun Alqur'ani kuma ya san wani abu game da Aljanu.
Na yi cikakken bayani akan wannan a cikin posting dina mai taken YADDA AKE YIN RUQIYYAH.

★JINNUL JALAB BISA SAKACI
Idan mutum yana aikin cire Aljanu kamar Ruqiyyah, to yana da kyau ya kasance yana kokarin zama da cikakken tsarki da kuma yawaita Azkar.
Domin duk Aljanin da ka qona to fa yana jin haushinka ne kuma zai qullace ka.
To idan Mai Ruqiyyah ko mai ba da maganin Aljanu yay sakaci da wadannan, Aljanun za su iya shiga jikinsa kai tsaye su kwantar da shi.
In kuma ba su samu dama ba sai su dinga 6atawa mutum magungunansa.
Misali idan ka ajjiye magani sai su zo su zuba maka wani abu a ciki.
Duk maganin da kasan idan ka baiwa mutane suna samun lafiya to yanzu in ka bayar sai kaga baya aiki ko kuma ya karawa mutum wata cutar.
Wannan yana cikin dalilan da suke sakawa ka ji Malami maganinsa yana da tasiri amma daga baya sai abin na sa ya ta6ar6are.

★JINNUL JALAB BISA SABO
Tana iya yiwuwa mai Ruqiyyah ko mai bada magani su saba da wandansu Aljanu saboda yanayin aiki har su dinga zuwa wajensa ko ma su zauna tare da shi. To shi ma muna kiransu Jinnul Jalab.
Misali, idan kai wa wani mutum Ruqiyyah, sai kaiwa Alajnin da yake jikinsa nasiha har ya musulunta. To bayan ya musulunta wannan Aljanin zai kasance yana qaunarka bayan ya dandani zaqin imani.
Ko ni akan kaina na samu Aljanu da yawa bayan sun musulunta a hannuna suna zuwa su kawo min ziyara ko su aiko min da gaisuwa.
Wadansu kuma dama musulmai ne amma saboda nay musu nasiha sai suke qaunata.
Da akwai Alajnun da in kuka saba ta wannan hanyar za su dinga koya maka yadda ake hada magani kuma za su dinga baka shawarwari akan yadda zakai aikinka.
To amma dai sai an lura sosai, domin ana samun kuskure da yawa.
Misali: Wani Aljani ya ta6a zuwa wajena ya ce sunansa Mallam Umar, ya ce ya dade yana samun labarina kuma yana so ya kawo min ziyara to amma ayyuka ne sukay masa yawa saboda a kullum yana samun Aljanu sama da miliyan daya wadanda suke zuwa wajensa domin su musulunta.
Sai na ce to ya karanta min inda ya iya a Alqur'ani.
Sai ya fara karanta "Muhammadur RasulUllahi, wallazhiyna ma'ahuw ashidda'u alal kuffari ruhama'u baynahum.......
"
Daga fara karatunsa kafin ya je karshe ya yi 6ata ya fi goma sha biyar.

Da na kure shi sai ya fara ba ni hakuri. Sai yay min bayani cewa gaskiya ba namiji bane. Ashe macece kuma makauniya ce, ba ta gani amma dai musulma ce.

Sannan wani Aljani ya ta6a zuwa wajena,  ya ce min sunansa Sheikh Ahmad. Wai shi ne shugaban Aljanun garin Madina gaba daya.
Sai na  ce yay min larafci sai ya kasa.
Da ya ga na kure shi sai ya ba ni hakuri, ya ce Sunansa Kingkong kuma shi arne ne ba musulmi ba.

To gaskiya na gamu da irin wadannan da yawa, wasu ma ba zan iya tunawa yanzu ba, wasu kuma mun saba da su sosai, daga baya da na kara samun ilmi duk na sallame su.
Kuma hatta a cikin Ruqiyyoyin dana tura muku ta whatsApp kun ji Aljanin da ya zo wajen wata yarinya ya ce ya zo ne ya wanke mata zuciyarta saboda tana qaunar Manzon Allah ﷺ amma dana kure shi sai ya ce shi kafuri ne ba ya salla.
Haka ma na saka muku Ruqiyyar wannan Aljanin wanda ya je wajen wata yarinya ya ce mata shi ne Manzon Allah ﷺ
kuma har ya bata sadakar gashinsa ya ce a dinga jikawa marasa lafiya.
Na san wadannan duk kun saurare su kai tsaye.

Don haka shawara musamman ga masu rukiyya kada wani Aljani ya zo ya ce muku shi mai taimako ne ku yarda da shi ko ku bar shi ya zauna ajikin mutum wai da sunan yana taimaka masa, na yi cikakken bayani akan wannan acikin posting dina mai taken YADDA AKE YIN RUQIYYAH.


Daga Sunnah Medicine,  Masu yin Ruqiyyah da harhada magunguna na Musulunci http://bashirhalilu.blogspot.com.

Lambar waya 08162600700

Comments

Post a Comment

Popular Posts