JINNUL KATFA

JINNUL KATFAH

Nau'in Aljanu taqadirai kuma masu tsatstsauran ra'ayi.

https://www.facebook.com/sunnahruqyah/

Jinnul Katfah wasu nau'in Aljanu ne manya-manya sosai, suna cikin gingima-gingiman Aljanu wadanda halittarsu ta fi ta 'DanAdam girma sosai.

Idan wani Aljanin kamar Jinnul Shu'un (Aljanin da tsawonsa bai wuce idon sawun mutum ba) ya shiga cikinsu to ba za su iya gane cewa akwai me rai a cikinsu ba.
.
Suna da manyan halitta sedai ba su da kwarin kafafuwa, ba sa iya jurewa tsayuwa.
.
Jinnul Katfa suna cikin nau'in Aljanun da ba sa rayuwa a cikin mutane, sedai sukan shiga cikin mutane lokaci zuwa lokaci sannan su koma inda suka fito.
Kuma basu da yawa a duniya saboda basa aure kuma basa bada aure sai a cikin jinsin su.
.
Jinnul Katfah kuma suna cikin nau'in Aljanun da sukan iya canjawa zuwa wata halittar.
.
Mafi yawan wadannan Aljanu Kafurai ne ba a fiye samun musulmi a cikinsu ba.
.
Jinnul Katfa suna zaune ne a cikin qanqara a can cikin Sahara.
.
A tsarin mulkin wadannan Aljanu dukkan Aljanin da ya haifi 'ya'ya talatin to dole ya tsayar da haihuwa haka. Domin ana iya samun Aljani mai mata dari uku da 'ya'ya dari bakwai ko sama da haka.

In kuwa Aljani ya haifi 'ya'ya sama da talatin a tsarin mulkin Jinnul Katfah to za a kasheshi, a kashe matansa da gabadayan 'ya'yansa sannan a rushe gidansa kuma in yayi wani abu wanda tarihi zai iya tunawa da shi duk sai a hada a qona su.
.
Duk Aljanin da matarsa ta haifi 'ya'ya biyu to dole su cinye daya su bar daya amma basa cin 'ya'yan wani sai na su.
.
Jinnul Katfah basa kaunar wani Aljani ya shiga masarautarsu ko ya ra6i inda suke. Duk kuwa wanda yay karambanin shiga cikinsu to za su kashe shi ne kowane irin Aljani ne.

Idan wani Aljani daga cikinsu yana so ya shiga cikin jinsin wasu Aljanun don yay wani uziri to dole ne ya sanar da sarkinsu. Zai fadi lokacin da zai tafi, da inda za shi da kuma lokacin da zai dawo.
.
Wadannan Aljanu basa son kallo. Domin koda cikin wanin jinsin wasu Aljanunsuka shiga to in Aljani ya fiye kallonsu ko ya nuna ya sansu sai su cutar da shi.
.
Idan wani Aljani daga cikin Jinnul Katfah ya gudu daga masarautarsu ya koma cikin wasu Aljanun to 'yan uwansa za su kamo shi su kashe shi. Don haka idan Jinnul Katfah ya musulunta ko ya canja masarauta to saidai inda ya koma su ba shi sarauta ya zama babba a cikinsu. Yadda zai kasance duk wanda ya ta6a shi to ya ta6o taron dangi ne, domin dukkan jama'ar Aljanun za su yaqe shi.
.
Jinnul Katfah sun tsani sauran jama'ar Aljanu, su ma jama'ar Aljanu sun tsane su. Yawanci ba abinda ke shiga tsakaninsu sai yaqe-yaqe.
.
YADDA MUTUM ZAI GANE JINNUL KATFAH YA SHAFE SHI.
.
★Akwai matsanancin ciwon kafa.

★ Idan suka buge mutum yana faduwa ya kasa tafiya. Domin mafi yawa su ne suke sa farfadiya.
.
★Idan ana Ruqiyya za ka ga basa iya hada ido da mai ruqiyyar.
.
★Idan Jinnul Katfah ya buge mutum za ka ga mutumin ya dantse idonsa baya budewa. Kodai akwai wasu Aljanun da suke yin haka bayan Jinnul Katfah
.
★Za ka ga mutum ya dartse haqoransa wani ma yana tauna harshensa jini yana zuba. Amma tabriyqul Jinni ma sukan yi haka.
.
★Jinnul Katfah suna dadewa ba su tashi a jikin mutum ba amma kuma in suka tashi abin yana yin muni sosai.
.
★Mai irin wadannan Aljanu za ka samu yana da zafin zuciya da mummunan riko. Kusan dukkan abinda akay masa mara dadi sai yace sai ya rama.
.
★ Jinnul Katfah suna cikin Aljanun da suke saka mutum ya ji sam baya son yay ibada kamar sallah da karatun Alqur'ani. Koda dai wasu Aljanun kamar Jinnul As'wad da Shaitanun mariyd suma suna sa haka.
.
★Za ka samu mutum yana son yin abu shi kadai, ba ya so kowa ya shigar masa. Kuma mutum ya fi son ya dinga zaunawa shi kadai ba cikin mutane ba. Amma Jinnuz Zulam suma suna sa haka kamar yadda mukay bayaninsu tintini.
.
★Idan Jinnul Katfah suka bige mutum za ka samu karfinsa ya nunku sosai. Domin koda mace ce wata sai sama da maza goma sun taru suke iya riqeta tana jefar da su.
.
Na ta6a yi wa wata yarinya mai irin wannan Aljanin Ruqiyyah. Sedai mutanen wajen sun sha mamaki saboda ni kadai na riqe shi bayan ta wahalar da taron samarin da suka taru akanta. Saboda sirrin shi ne goshin mutum kawai ake kamawa a riqe. Shikenan Aljanin ya dauru. Sedai ya dinga ba ka hakuri. Amma don an daddaure mutum da igiya ko an daddane shi wannan ba zai hana Aljanin tasiri ba.
.
★ Yara ko kuma mutanen da suke da Jinnul Katfah za ka samu ba sa jin duka. Domin duk dukan da zakaywa mutum za ka ga ya warware cikin kankanin lokaci kamar ba shi aka kusa kashewa ba. Musamman yaran da basa son makaranta, in an ga dukan bai canja su ba to sai a sake dabara.
.
★Mutanen da suke da Jinnul Katfah a jikinsu za ka samu ba su da tsoro. Domin ka iya ganin mace da tsakar dare ta tashi ta bude kofar gida ta fita waje tay tafiya mai nisa koma tabar garinsu zuwa wani garin ita kadai ba tare da jin tsoro ba kuma a kafa.
.
Da dai alamomi da yawa.
.
.
Da akwai wani audio na hira da mukay da wata Aljana akan rayuwar Jinnul Katfah. Zan duba idan na gan shi zan dora muku shi a whatsApp insha Allahu.
.
Muna sane da alkawarinmu akan bayanin Tabriyqul Jinni: wato Aljanu mashaya jini. Masu sakarwa mata jini.
.

WhatsApp & call 08162600700, 08134434846.

Comments

Popular Posts