GURAREN ZAMAN AL-JANU ACIKIN GIDAJEN MUTANE

GURAREN ZAMAN AL-JANU ACIKIN GIDAJEN MUTANE.

Da yadda ake korarsu.

Daga cibiyar Tarbiyyah  Islamiyyah, masu yin Ruqiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.


Kamar yadda kowa ya sani cewa Aljanu suna da guraren zama da yawa, kamar yadda wannan shafi na t.me/tarbiyyahislamiyyah ya sha kawo bayanai akai.

Kamar Sahara, Maqabarta, Cikin kogi,  cikin kogo,  kan bishiyoyi,  cikin ramuka da kwazazzabai,  jikin mutane, gonaki, Masallatai, cikin daji, cikin rijiyoyi,  kan bola, mayanka, da dai sauransu.
Karanta cikakken bayanin akan guraren zaman Aljanu acikin wannan shudin rubutun.

https://plus.google.com/+BashirHalilu/posts/g1hsZwUaGNx

A yanzu haka zamu yi karin bayani ne akan GURIN ZAMAN AL-JANU NA CIKIN GIDAN MUTANE.

HUJJAR DA TAKE TABBATAR DA CEWA AL-JANU SUNA SHIGA GIDAJEN MUTANE

حَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ، حَدَّثَنَا يَعْقُوبُ وَهُو ابْنُ عَبْدِ الرَّحْمَنِ الْقَارِيُّ، عَنْ سُهَيْلٍ، عَنْ أَبِيهِ، عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ، أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ مَقَابِرَ، إِنَّ الشَّيْطَانَ يَنْفِرُ مِنَ الْبَيْتِ الَّذِي تُقْرَأُ فِيهِ سُورَةُ الْبَقَرَةِ»

Ma'ana

An kar6o daga Aba Hurairata,  Allah Ya kara yarda a gare shi,  ya ce "Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ce "Kada ku mayar da gidajenku maqabartu,  (gurinda ba a karanta Alqur'ani) domin hakika Shaidan yana guduwa daga gidanda ake karanta Suratul Baqarah"

Wannan Hadisi ya kawo bayani akan  Shaidanun Aljanu suna shiga gidajen mutane da kuma yadda ake korarsu.

Hadisi na biyu.

Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya ce: "Idan dare ya shiga ko kuma kun yamma ta, to ku kame kananan `ya`yanku, domin awannan lokacin ne shaidanu suke yaduwa amma idan aka sami kimanin awa daya to kwa iya sakin yaranku kuma idan zaku kwanta ku rufe kofofinku, idan zaku rufe ku ambaci sunan ALLAH. domin Shaidan ba ya iya bude kofar da aka rufe ta (da sunan Allah).

Kuma ku kife qorukan ku. (jam'in Qwarya),  ku ambaci sunan ALLAH yayin da zaku kife kuma ku rufe tukwanan ku, ku ambaci ALLAH lokacin da zaku rufe din, ko da wani abu ne ku dora akai kuma idan zaku kwanta bacci ku kashe wuta"

(Sahih Muslim).

ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ :
ﻭﺣﺪﺛﻨﻲ ﺇﺳﺤﺎﻕ ﺑﻦ ﻣﻨﺼﻮﺭ .
ﺃﺧﺒﺮﻧﺎ ﺭﻭﺡ ﺑﻦ ﻋﺒﺎﺩﺓ . ﺣﺪﺛﻨﺎ
ﺍﺑﻦ ﺟﺮﻳﺞ . ﺃﺧﺒﺮﻧﻲ ﻋﻄﺎﺀ؛ ﺃﻧﻪ
ﺳﻤﻊ ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻳﻘﻮﻝ :
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ : ‏( ﺇﺫﺍ ﺟﻨﺢ ﺍﻟﻠﻴﻞ - ﺃﻭ
ﺃﻣﺴﻴﺘﻢ - ﻓﻜﻔﻮﺍ ﺻﺒﻴﺎﻧﻜﻢ . ﻓﺈﻥ
ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻳﻨﺘﺸﺮ ﺣﻴﻨﺌﺬ . ﻓﺈﺫﺍ
ﺫﻫﺐ ﺳﺎﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻓﺨﻠﻮﻫﻢ .
ﻭﺃﻏﻠﻘﻮﺍ ﺍﻷﺑﻮﺍﺏ . ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ
ﺍﻟﻠﻪ . ﻓﺈﻥ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻻ ﻳﻔﺘﺢ ﺑﺎﺑﺎ
ﻣﻐﻠﻘﺎ . ﻭﺃﻭﻛﻮﺍ ﻗﺮﺑﻜﻢ . ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ
ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ . ﻭﺧﻤﺮﻭﺍ ﺁﻧﻴﺘﻜﻢ .
ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﺍﺳﻢ ﺍﻟﻠﻪ . ﻭﻟﻮ ﺃﻥ
ﺗﻌﺮﺿﻮﺍ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺷﻴﺌﺎ . ﻭﺃﻃﻔﺆﺍ
ﻣﺼﺎﺑﻴﺤﻜﻢ.

Daga wannan hadisi za mu fahimci cewa Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana umartarmu mu da mu rufe kayan amfaninmu idan zamu kwanta bacci sannan mu rufe kofa kuma mu kashe fitila.

Da akwai nau'in jinnu masu zuwa su dauki kayan mutane suyi amfani da su,  na kawo bayaninsu acikin rubutuna mai taken JINNUL SHU'UN,  mai bukata zai iya dubawa ya karanta. Hakanan Hadisin yana nuna mana cewa in an rufe kofa Shaidan ba aya iya budewa, to ashe in ba a rufeta da sunan Allah ba zai bude kenan. Haka nan yana karantar da mu kashe fitila idan za mu kwanta barci,  saboda idan Aljanu sun fito yawo da daddare duk inda suka hango hasken fitila can suke fara dosa.

IDAN AL-JANU SUN SHIGA GIDAN MUTANE A INA SUKE TAREWA?

Guraren zaman Aljanu acikin gidajen mutane guda uku ne, kamar yadda mu ka fada tunda farko

(1) DUKKAN WAJEN DA AKE AJJIYE ABINCI KO AKE CIN ABINCI.

Babu shakka Aljanu suna zama a gurin da abincin mutanen gida yake kuma suna zuwa suna satar musu abincin domin su ciyar da iyalansu, kamar yadda ya zo acikin shahararriyar qissar nan ta Sahabin Manzon Allah (SAW).

An kar6o daga Aba Hurairata Allah ya kara yarda a gareshi, ya ce " Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Ya wakiltani in kula da zakkar watan Azumin Ramadana. Sai ga wani ya zo yana satar abincin (da nake gadi).
Sai na kama shi, na ce Sai na kai ka wajen Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ .
Sai ya ce min "WAllahi ni mabukaci ne kuma ina da iyali da yawa ga kuma tsananin bukata"
Sai na rabu da shi.
Da gari ya waye sai Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Ya ce "Ya kukai da bakonka na jiya?"
Sai na ce Ya Ma'aikin Allah, ya koka min tsananin bukata da kuma yawan iyali. Sai na tausaya masa na kyale shi.
Sai Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Ya ce "Karya yake kuma zai dawo".

Saboda haka sai nay tarkonsa.
Sai kuwa gashi ya dawo yana satar abincin. Sai na kama shi, na ce to wAllahi sai na kai ka wajen Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Domin karo uku kenan ina kama ka. Se kay rantsuwa ba za ka dawo ba sai kuma ka dawo.
Sai ya ce "To ka kyale ni se in koya maka wasu kalmomi wadanda Allah zai sa ka amfana da su".
Sai na ce Wadanne ne?
Sai ya ce "Idan ka je wajen kwanciyarka, ka karanta Ayatal Kursiyyu har karshen ayar. To Akwai me gadi da Allah zai saka maka kuma Shaidan ba zai iya kusantarkaba har sai ka wayi gari".
(Da Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻲ ﻭﺳﻠﻢ
Ya ji haka sai ya ce "Amma fa shi (wannan mai zuwar maka da daddaren) makaryaci ne, sai dai gaskiya ya gaya maka. Ya Aba Hurairata ka san ko da wa kake gamuwa har sau ukun nan?"
Sai na ce A'a.
Sai ya ce "Shaidan ne"
.
.
Wannan qissa tana tabbatar mana da cewa Shaidanu suna zama a inda abincin mutane yake, har suna kai hannuwansu, suna diba.

    (ii) Haka nan dukkan inda mutane suka zauna suna cin abinci, Aljanu suna zuwa, kamar yadda ya zo a Hadisin Manzon Allah (SAW)

عن أنس رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان إذا أكل طعاماً لعق أصابعه الثلاث، قال: وقال: (( إذا سقطت لقمة أحدكم، فليمط عنها الأذى، وليأكلها، ولا يدعها للشيطان . وأمر أن تسلت القصعة قال: فإنكم لا تدرون في أي طعامكم البركة)) رواه مسلم.
Ma'ana.

An kar6o daga Anas Allah Ya kara yarda a gareshi,  ya ce "Manzon Allah صلى عليه وسلم
ya ce "Idan lomar dayanku ta fadi (yayin da yake cin abinci), to ya cire dattin da yake jiki, ya ci. Kada ya barwa Shaidan ita... " izuwa karshen Hadisin.
Mislim ne ya ruwaito.

Wannan Hadisi ya tabbatar mana da cewa Aljanu suna zaunawa a inda mutane suke cin abinci kuma idan loma ta fadi suna dauka.

Shi yasa ya wajaba mutum ya karanta wannan addu'a yayin da zai fara cin abinci,  kamar yadda ya zo a Hadisi


روته عائشة رضي الله عنها أن النبي صلى الله عليه وسلم قال : ( إِذَا أَكَلَ أَحَدكُمْ طَعَامًا فَلْيَقُلْ بِسْمِ اللَّه , فَإِنْ نَسِيَ فِي أَوَّله فَلْيَقُلْ : بِسْمِ اللَّه فِي أَوَّله وَآخِره ) رواه الترمذي (1781) وصححه الشيخ الألباني رحمه الله .

Ma'ana.

Nana A'isha Allah Ya kara yarda a gareta,  ta ruwaito cewa Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ce "Idan dayanku zai ci abinci,  to ya ce Bismillah. In kuma ya manta bai fada a farko ba,  to ya ce Bismillahi fiy auwalihiy wa akhirihyi".
Tirmiziy ne ya ruwaito.

Malamai su ka ce,  idan mutum ya fara cin abinci bai ambaci Allah ba to tare da Shaidan suke ci amma idan ya tuna kuma ya ambaci Allah daga baya sai Shaidanin ya amayar da abinda ya ci.

       Sannan dukkan wajen da aka ci abinci, aka zuzzubar akasa, ba a share ko an kwashe ba, to shi ma Aljanu suna zuwa, domin su tsinci abnida za su ci.

Saboda haka indai ana so a rabu da Aljanu daga cikin gida to ya wajaba adinga tsaftace inda ake ajjiye abnici ko cin abinci kuma a dinga ambaton Allah kamar yadda sunnah ta koyar.

Aljanun da suke satar kayan mutane, masu Ruq'yah suna kiransu da suna SARIQUL JINNI. Na kawo cikakkun bayanai akansu har sau biyu acikin shafina na face book (Bashir Halilu Tarabiyah Islamiyyah) in ka duba zaka same shi.


       Karin bayani anan shi ne, yana da kyau mutane su fahimci cewa, Shaidanun Aljanu suna iya zuwa su zubawa mutum guba a abincinsa, a yayin da ya ajjiye shi a bude, ba tare da ya ambaci sunan Allah ba ko kuma su ci, su rage masa.  Don haka a shawarce, ya kamata mutane su daina bude abinci kuma su tafi su barshi da niyyar ya huce, idan ma an yi hakan to yana da kyau a sake dumamawa kafin a ci, saboda in ma sun zuba maka wata guba zata kone sannan idan kwayoyin cuta sun shiga abincin su ma za su kone da yaddar Allah.

(2)NA BIYU.
     DUKKAN GURIN DA AKE BUDE TSARAICI ACIKIN GIDA.

      Gurin zaman Aljanu na biyu acikin gidan mutane shi ne dukkan gurin da mutane suke bude tsaraicinsu.

Dukkan inda ake bude tsaraici tabbas Shaidanun Aljanu suna zuwa, wannan shahararren al'amari ne wanda kowa ya sani. Shi yasa duk wani waje da Aljani ya san cewa in ya je zai ga tsaraicin mutane to yana wajen, koda ba cikin gidan mutane bane.

Wannan ce tasa suke zuwa gidajen biki da guraren da ake kida da rawa da filayen da ake ball da makarantun kwana na yanmata da dai duk inda suka san cewa mutane suna bude tsaraicinsu da tare da suturcewa ko jin kunyar junansu ba. Koda a waya ne mutum yake kallon tsaraici ko tv,  to Aljanu suna zuwa su kewaye shi,  su dinga kallo tare,  karshe kuma su kima jikinsa.

Acikin gidajen mutane dai, sun fi zama a irinsu:

      ( i ) Bandaki.
          Wannan dalili ne yasa Shaidanu da suke zama a gidajen mutane, suka za6i su zauna a bandaki, don kallon tsaraici.

   Shi yasa Manzon Allah (SAW) ya umarcemu da yin addu'a, yayin shiga bandaki da fitowa.

عن أنس رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا دخل الخلاء قال: ((اللهم إني أعوذ بك من الخُبث والخبائث))؛ أخرجه السبعة.

Ma'ana.

An kar6o daga Anas Allah Ya kara yarda a gareshi,  ya ce "Manzon Allah صلى الله عليه عليه وسلم
ya kasance,  idan zai shiga bandaki yana cewa "Ya Allah ka tsareni daga sharrin Aljanu maza da Aljanu mata".

Malaman Hadisi bakwai duka sun ruwaito shi,  wadanda suka hada da Bukhari da Muslim.

     Kai tsaye wannan Hadisi yana nuna mana cewa lallai akwai Aljanu acikin bandaki kuma ya bamu addu'ar neman tsari daga sharrinsu.

        A wani Hadisin kuma.

عن علي رضي الله تعالى عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال : ( ستر ما بين أعين الجن وعورات بني آدم إذا دخل الكنيف أن يقول باسم الله ) رواه الترمذي.

Ma'ana.
An kar6o daga Aliyyu Allah ya kara yarda a gare shi,  ya ce Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ce

"Abinda ke tsakanin tsaraicin dayanku da idanun Aljanu in ya shiga bandaki,  shi ne ya ce Bismillahi".

Tirmiziy ne ya ruwaito shi.

    Kenan in bai ce Bismillahi ba,  Aljanu suna kallon tsaraicinsa.

        Ba kallon tsaraicin mutane kawai irin wadannan Aljanu suke yi ba, suna ma iya shiga jikin mutum, su dinga saduwa da shi ko su saka masa cuta. Shi yasa manzon Allah (SAW) ya koyar da mu ladabai da yawa na ta'ammuli da bandaki ko kuma dukkan wajen da ake bude tsaraici. Akwai babuka da yawa da manyan Malamai su ka yi akan "Ladaban biyan bukata", yana da kyau ace kowa ya sansu kuma ya fahimce su.

     Nau'in Aljanun da suke zama a cikin bandaki muna kiransu da suna KHADIMUL HAMMAM, na kawo cikakken bayani akansu da yadda ake gane cewa akwaisu acikin bandaki da kuma yadda ake maganinsu. za ku iya samu a shafukana idan ku ka duba bashirhalilu.blogspot.com.

 
       (ii) Haka nan dukkan shinfidar da ake kwanciyar jima'i.

       Shi ma waje ne da Shaidanun Aljanu suke zuwa. Shi yasa Manzon Allah (SAW) ya koyar da mu addu'a, yayin hawa shimfidar aure.

روى البخاري (6388) ومسلم (1434) عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : ( لَوْ أَنَّ أَحَدَهُمْ إِذَا أَرَادَ أَنْ يَأْتِيَ أَهْلَهُ قَالَ بِاسْمِ اللَّهِ اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ وَجَنِّبْ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا ، فَإِنَّهُ إِنْ يُقَدَّرْ بَيْنَهُمَا وَلَدٌ فِي ذَلِكَ لَمْ يَضُرَّهُ شَيْطَانٌ أَبَدًا ).

وفي رواية للبخاري (3283) ( لَمْ يَضُرَّهُ الشَّيْطَانُ وَلَمْ يُسَلَّطْ عَلَيْهِ ) .

Ma'ana.
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Ibn Abbas Allah Ya kara yarda a garesu cewa "Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ce

"Da ace dayanku lokacin da yay nufin zuwarwa iyalinsa (don jima'i)  zai ce "Ya Allah ka nisantar da mu daga Shaidan kuma ka nisantar da Shaidan daga abinda zaka azurtamu (na haihuwa), to in an kaddara za su samu haihuwa a wannan saduwar, Shaidan ba zai ta6a cutar da shi ba har abada".

A ruwayar Bukhari kuma "Shaidan ba zai iya cutar da shi ba kuma ba za a ba shi iko akansa ba".

     Daga wannan Hadisi za mu fahimci cewa lallai Shaidan yana zuwa lokacinda ake saduwa,  domin ya samu damar saka rabonsa acikin abinda za haifa tun daga lokacin saduwa,  amma in aka ambaci Allah to ba ya samun dama.

  Shaidani ya kan zo yayin saduwar aure, ya zama shi ne yake saduwa da matar, ba mijinta ba ko kuma ya zama shi mai gidan da Aljana yake saduwa, ba matarsa ba. Ya kan iya kasancewa kuma ya zama su ukun suke saduwar, wato da mijin da matar da kuma Aljanin. Nau'in Aljanu da suke saduwa da matan mutane ana kiransu JIINUL ASHIQ. Na yi cikakken bayani akansu acikin shafuka na, za ka iya dubawa domin ganin ta hanyoyin  da zaka iya gane cewa Aljani yana kawo ziyara shimfidar aurenku da kuma yadda ake maganinsa da yaddar Allah.

   (iii) Sannan dukkan gurinda ake canja tufafi.

          Kamar yadda bayani ya gabata cewa suna zama ne a inda ake bude tsaraici, to hatta kaya idan DanAdam zai canja, su kan zo su kewaye shi don kallon tsaraicinsa. Shi yasa Manzon Allah (SAW) ya koyar da mu addua'a, yayin da zamu cire tufafi da kuma bayan mun saka.

عن أنس بن مالك رضي الله عنه : قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : ( سِتْرُ مَا بَيْنَ أَعْيُنِ الْجِنِّ ، وَعَوْرَاتِ بَنِي آدَمَ إِذَا وَضَعُوا ثِيَابَهُمْ أَنْ يَقُولُوا : بِسْمِ اللَّهِ ) .

Ma'ana.
    An kar6o daga Anas Allah Ya kara yarda a gare shi,  ya ce, Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya ce

    "Abinda yake kare tsakanin idanun Aljanu da tsaraicin `yan Adam idan sun cire kayansu,  shi ne su ce Bismillahi".

        Wannan Hadisi yana nuna mana cewa duk wanda ya cire kayansa ba tare da ya ambaci sunan Allah ba to Aljanu suna kallon tsaricinsa.

     Ba kallo kawai Shaidanu sukewa tsaraicin mutane ba, Shaidanu sun kasance ta tsaraici suke shiga jikin mutane. Wannan yana daya daga cikin dalilai da su ka sa Aljanu suka fi shiga jikin mata, ba kamar maza ba. Saboda mata sun fi maza wulakanta tsaraicinsu, su kuma sai su shige musu, su saka musu cututtuka kuma su dinga zuwa suna saduwa da su. Muna kiransu JINNUL ASHIQ.


       (3) DUKKAN GURIN DA AKE ZUBAR DA KAZANTA.

     Dukkan wajen da ake barin kazanta ko bola acikin gida, to Aljanu suna zama a wajen. Haka nan jikin Dan-Adam, idan mutum yana zama da kazanta, kamar rashin wanka ko wanki ko zama da janaba, da sauran gurare kamar

( i ) Bandaki.
     Bandaki wajen kazanta ne,  don haka ya zama wajen zaman Aljanu,  kamar yadda mu ka kawo Hadisi a sama.

     ( ii ) Gurin da ake daure dabbobi.
         Saboda fadin Manzon Allah (SAW).

    
حَدَّثَنَا مُوسَى بْنُ إِسْمَاعِيلَ ، حَدَّثَنَا عَمْرُو بْنُ يَحْيَى بْنِ سَعِيدٍ ، قَالَ : أَخْبَرَنِي جَدِّي ، عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ : أَنَّهُ كَانَ يَحْمِلُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِدَاوَةً لِوَضُوئِهِ وَحَاجَتِهِ ، فَبَيْنَمَا هُوَ يَتْبَعُهُ بِهَا ، فَقَالَ : مَنْ هَذَا ؟ فَقَالَ : أَنَا أَبُو هُرَيْرَةَ ، فَقَالَ : ابْغِنِي أَحْجَارًا أَسْتَنْفِضْ بِهَا ، وَلاَ تَأْتِنِي بِعَظْمٍ وَلاَ بِرَوْثَةٍ . فَأَتَيْتُهُ بِأَحْجَارٍ أَحْمِلُهَا فِي طَرَفِ ثَوْبِي ، حَتَّى وَضَعْتُهَا إِلَى جَنْبِهِ ، ثُمَّ انْصَرَفْتُ حَتَّى إِذَا فَرَغَ مَشَيْتُ ، فَقُلْتُ : مَا بَالُ العَظْمِ وَالرَّوْثَةِ ؟ قَالَ : هُمَا مِنْ طَعَامِ الجِنِّ ، وَإِنَّهُ أَتَانِي وَفْدُ جِنِّ نَصِيبِينَ ، وَنِعْمَ الجِنُّ ، فَسَأَلُونِي الزَّادَ ، فَدَعَوْتُ اللَّهَ لَهُمْ أَنْ لاَ يَمُرُّوا بِعَظْمٍ ، وَلاَ بِرَوْثَةٍ إِلَّا وَجَدُوا عَلَيْهَا طَعَامًا

Ma'ana.
     An kar6o daga Abu Hurairah Allah Ya kara yarda agare shi cewa: Ya kasance yana dauke da butar ruwa domin Alwalar Manzon Allah  صلى الله عليه وسلم
da kuma biyan bukatunsa.  Sai Watarana Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
ya zagaya domin biyan bukatarsa, Sai ya tambaya:

"Shin wanene wannan?"

Na ce "Abu Hurairah ne".
 
Sai yace "Ka taho min da duwatsu, in yi tsarki da su amma kada ka kawo min Qashi ko kashin dabba".

    Sai na taho masa da duwatsu ina dauke dasu acikin tufafina. Har sai da na ajiyesu agefensa. Sannan na juya. Har sai da ya kammala, Sai na tafi tare dashi.

Sai nace masa "Menene laifin Qashi ko kashin dabbobi?".

  Sai yace min "Su biyun suna cikin abincin Aljanu. Domin jama'ar Aljanu Nasibina, sun zo gareni, madalla da wadannan Aljanu.
Sai su ka tambayeni guzuri na abinci. Sai na roki Allah cewa kada su wuce Qashi ko kashin dabba face sai sun samu abinci ajikinsa".

Bukhari ne ya ruwaito.

       Wannan Hadisi yana nuna mana cewa Aljanu suna samun abinci ajikin kashin dabbobi,  don haka dukkan inda ake daure dabbobi agidajen mutane, to Aljanu suna zama,  domin samun abinci.

     A wani Hadisin kuma yana nuna cewa su Aljanun suna cin Qashin dabbobin ne,  su kuma dabbobin Aljanun sai su ci kashin dabbobin mutane.

     (iii) Wajen da mutanen gida suke zuba shara.
      Domin Aljanu suna zuwa su tsinci guntayen Qashi da sauran abinci kuma a wajen suke yin walimarsu. Shi yasa ake so a ambaci Allah idan za a zubda qazanta acikin shara.

    (iv) Inda mata suke ajjiye tsummokaran da suke qunzugu da su. Akan samu shaidanu wadanda su kuma mashaya jini ne, don haka suke bin inda mata suke ajjiye tsummokar kunzugu ko zubar da audugar da su ka yi amfani da ita. Irin wadannan Aljanu ana kiransu Tabriyqul jinni.
  Suna suna zama ne a duk inda ake ta'ammuli da jini kamar mayankar dabbobi da dai sauransu,  ba kawai sai jinin mata ba.

YADDA AKE GANE AKWAI AL-JANU ACIKIN GIDA:-
.
Yawan jin sallama ko takun kafafu ko maganganu da kwaramniya ba tare da an ga kowa ba.
.
Yawan ganin wani mutum ko mace ko wata dabba zaune a cikin gida ko bandaki,  daga baya kuma a nemesu a rasa.
.
Yawan 6atan kaya kuma a rasa wanda ya dauka, sai lokacin da ba ka bukatar sa kuma sai ka gan shi.
.
Yawan ganin an hargitsa ma ka kaya ko an yi ma ka bincike kuma ka rasa kowaye.
.
Yawan 6acin rai ko faduwar gaba idan ka na cikin gida amma in ka fita sai ka daina ji ko mace ta dinga jin kamar ta hada kayanta ta fita daga gidan.
.
Yawan tsagewar wata katanga a cikin gida kuma duk gyaran da za a yi sai ta kuma darewa. Haka na faruwa ne idan sun mayar da wajen hanyar shigowarsu.
.
Yawan ganin wata dabba ta gifta kamar maciji ko kare dds kuma in an duba sai a rasa inda ya shiga.
.
Yawan jin dudubniya ko kokaye-kokaye a saman daki.
.
Yara su dinga firgita cikin dare.

Da dai alamu da yawa.

  Shiga wannan shudin rubutun ka sauke Application dinmu a wayarka, wanda zaka dinga samun rubututtukanmu a duk sanda mu ka yi su. Application din yana da saukin amfani kuma zai dinga ba ka sanarwa, a duk lokacin da mu ka dora sabon rubutu akansa.

http://www.appsgeyser.com/7550770

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruq'yah da harhada Magugunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Comments

  1. Jazaakumullaahu khairan sheikh,,,,daga Murtala Abubakar kubwa,Abuja. Muna matukar karuwa da Wannan bayanai kuma yana temaka mini agurin ruqyah danakeyi.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular Posts